16 Nuwamba 2019 - 09:07
Hizbullah:Amurka Na Kokarin Zartar Da Shirinta A Kasar Labnon

Kungiyar Hizbullah ta ce Amurka da kawayenta na kokarin amfani da boren al'ummar kasar domin zartar da shirinta a kasar Labnon.

(ABNA24.com) Kungiyar Hizbullah ta ce Amurka da kawayenta na kokarin amfani da boren al'ummar kasar domin zartar da shirinta a kasar Labnon.

Shugaban Majalisar zartarwa na kungiyar Hizbullah Sheikh Ali Damoush ya bayana cewa da dama daga cikin bukatun masu zanga-zanga, hakkinsu ne, domin hakan ya biyo bayan matsalar tattalin arzikin da al'umma ke fuskanta sakamakon rashin adalci na shugabani da kuma yadda cin hanci da rashawa ya yi kamari a kasar, to amma bai kamata ba, a yi amfani da wannan dama wajen cimma manufofi na siyasa ba.

Sheikh Ali Damoush ya kara da cewa Amurka da kawayenta nason zartar da wani shiri na siyasa ta hanyar kakabawa kasar takunkuman tattalin arziki wanda zai yi sanadiyar hana zuba jari ga kamfanonin kasashen waje a kasar Labnon.



/129